logo

HAUSA

An yi shawarwarin kasa da kasa a Tanzaniya kan damammakin da Sin ke samarwa ta zurfafa yin kwaskwarima a sabon zamani

2024-07-24 15:44:49 CMG Hausa

 

Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da shawarwarin kasa da kasa a birnin Dares Salaam, fadar mulkin kasar Tanzaniya, kan damammakin da Sin take samarwa duniya daga matakin zurfafa yin kwaskwarima da ta gudanar a sabon zamani. Mahalarta taron fiye da 40, ciki hadda wakilan ofishin jakadancin Sin dake Tanzaniya da manyan kafofin yada labaran Tanzaniya da masana da sauransu, sun yi mu’ammala da shawarwari kan ma’ana mai zurfi da cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwamins ta Sin karo na 20, da damammakin da Sin take samarwa duk fadin Afrika wajen aiwatar da tsarin zamanintar da al’ummarta da sauransu.

A jawabin da ya yi ta bidiyo, shugaban CMG Shen Haixiong ya ce, kasancewar wani muhimmin bangare na yin kwaskwarima a gida a duk fannoni, tsarin zamanintar da al’ummar Sinawa na samun bunkasuwa har da samar da makoma mai haske nan gaba, yayin da Sin take kokarin yi wa kanta kwaskwarima. Ya ce CMG na dukufa kan ba da nagartattun labarai kan yadda Sin take gudanar da irin wannan kwaskwarima da zamanintar da al’ummarta, tana kuma kokarin kafa wata gada mai kyau ta kara mu’ammala da koyi da juna tsakanin Sin da kasashen duniya.

Babban darektan cibiyar dunkulewar matasan Afrika, kana shahararren masanin tattalin arziki na Afrika Francis Alexander Matambalya ya nuna cewa, kasashen Afrika na matukar bukatar daga karfinsu na daidaita harkokin kasashensu, kuma ci gaban da Sin take samu ya zama musu abin koyi. More damammakin da Sin take samarwa daga kwaskwarimar da take gudanarwa, na da muhimmanci ga bunkasuwar nahiyar Afrika nan gaba. (Amina Xu)