logo

HAUSA

Masana’antu a Najeriya sun yi asarar naira tiriliyon 1.7 a shekara guda kacal

2024-07-24 10:45:34 CMG Hausa

 

Shugaban hukumar tara kudaden shiga na cikin gida a tarayyar Najeriya Mr. Zacch Adedeji ya tabbatar da cewa, masana’antun dake kasar sun yi asarar tsabar kudi har naira tiriliyon 1 da dubu dari bakwai a cikin shekara guda sakamakon tsadar kudin musaya wanda ya tilasta masu dakatar da aiki, wasu kuma suka bar kasar.

Ya tabbatar da hakan ne a farkon wannan mako a birnin Abuja lokacin da yake jawabi gaban kwamitin kudi na majalissar dattawa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ya ce, duka wannan asarar masana’antun sun yi ta a shekarar bara, lamarin da ya shafi gwamnati matuka ta fuskar karbar kudaden haraji daga irin wadannan kamfanoni. Inda ya ce, a sakamakon wannan hali da masana’antun suka shiga za a dauki shekaru biyar zuwa goma gwamnati ba za ta rinka amfana ba ta fuskar kudaden shiga har sai lokaci da suka fara murmurewa.

Shugaban hukumar tara kudaden shigar a tarayyar Najeriya ya ce, kamfanonin ’yan kasashen waje da dama, musamman ma na makamashi da na magunguna sun bar Najeriya ne tun farkon hawan wannan gwamnati, da yawa dai sun alakanta wannan matakin da suka dauka kan tsadar kudaden musaya na kasashen waje da kuma karyewar darajar naira, yayin da wasu kamfanonin kuma suka danganta dakatar da harkokinsu a Najeriya saboda matsalar tsaro da karancin ciniki. (Garba Abdullahi Bagwai)