logo

HAUSA

Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda 125 cikin mako guda

2024-07-20 16:11:47 CMG Hausa

 

Kakakin rundunar sojojin Najeriya Edward Buba, ya ce a kalla mayaka 125 da ake zargi da ayyukan ta’addanci, dakarun sojin kasar suka hallaka a cikin mako guda, sakamakon wasu samame daban daban da rundunar ta aiwatar.

Edward Buba, wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a, yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce baya ga wadanda sojojin suka hallaka, sun kuma cafke ‘yan ta’adda sama da 200.

Kaza lika sun yi nasarar kubutar da mutane 140 da aka yi garkuwa da su, baya ga muggan makamai 120, da albarusai 1,793, da motoci 6, da babura 11, da kekuna 5, da dai sauran abubuwan amfani da suka kwato daga ‘yan bindigar.  (Saminu Alhassan)