logo

HAUSA

‘Yan takarar hamayya sun taya Kagame murnar lashe zaben shugaban kasar Rwanda

2024-07-19 10:30:36 CMG Hausa

‘Yan takarar hamayya na zaben shugaban kasar Rwanda da aka kammala a baya bayan nan, sun taya shugaba mai ci Paul Kagame na jam’iyyar RPF da ke kan karagar mulkin kasar, murnar lashe zaben.

Sakamako na farko-farko da hukumar zaben kasar ta fitar a jiya Alhamis ya nuna cewa, Paul Kagame ya samu kaso 99.18 na kuri’un da aka kada a zaben na ranar Litinin.

Dan takara na jam’iyyar hammaya ta Democratic Green Party of Rwanda Frank Habineza ya samu kaso 0.50 yayin da dan takarar Indipenda Philippe Mpayimana, ya samu kuri’u 0.32.

Paul Kagame mai shekaru 66 ya dare karagar shugabancin kasar a shekarar 2000. Ana jinjina masa saboda yadda ya jagoranci yakin ‘yantar da kasar ta rundunar RPA, wadda rundunar sojin RPF ne da ta kawo karshen kisan kare dangi da aka yi wa ‘yan kabilar Tutsi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin miliyan1. Haka kuma yunkurin RPF din ya kai ga farfado da zaman lafiya da hadin kai a kasar bayan kisan da ya shafe kwanaki 100.

Da yake jawabi ga wani taron manema labarai kwana 1 kafin zaben, Kagame ya ce babban abun da za a sa a gaba bayan zaben shi ne, ci gaba da samun nasarori a bangarorin tsaro da zaman lafiyar kasar tare da ci gaban harkokin zaman takewa da tattalin arziki. (Fa’iza Mustapha)