logo

HAUSA

Najeriya za ta fara sayar da tattaccen man fetur ga kasashen duniya nan da watan Disambar 2024

2024-07-18 10:14:50 CMG Hausa

Shugaban kamfanin mai na NNPC a tarayyar Najeriya Mr Mele Kyari ya ce, bisa yadda alamomi ke nunawa na tagomashin da Najeriya ke samu a kan sha’anin mai da iskar gas, zuwa watan Disambar bana, kasar za ta shiga cikin jerin kasashen da suke cinikin tattaccen mai a duniya.

Ya tabbatar da hakan ne a fakon wannan mako a lokacin da yake jawabi gaban kwamitin majalissar dattawa a kan harkokin kudi. Ya ce, yanzu haka gwamnati ta fara ganin haske daga irin sauye-sauyen da take yi a bangaren makamashin man fetur da iskar gas a kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban kamfanin mai na NNPC wanda yake tare da ministan kudi da takwaransa na kasafi da tsare-tsare da karamin minista a ma’akatar man fetur da kuma gwamnan babban bankin Najeriya Mr Olayemi Cardoso.

Ya ce, irin wadannan alamu sun hada da farfadowar matatar mai ta Fatakwal wadda za ta fara aikin cikin watan gobe, sai ta Warri da ita ma ake sa ran za ta dawo aiki a watan Satumba, sai kuma ta Kaduna wadda za ta fara aiki gadan gadan a cikin watan Disambar wannan shekara.

Mr Mele Kyari ya ci gaba da cewa, nan da ’yan watanni kalilan mizanin adadin hakar man Najeriya zai karu zuwa ganga miliyan 2 a rana saboda a tanadi dukkan kayayyakin da za su tabbatar da wannan buri.

A kan bukatun cikin gida kuwa, shugaban kamfanin man na NNPC ya shaidawa ’yan kwamitin cewa, “muna da wadataccen mai da muka samar a kasar, kuma muna kara tabbatar da ci gaba da tunkudo man duk kuwa da kalubalen da muke fuskanta wadanda suka kunshi fasa-kaurin man da ake yi ta kan iyakoki, amma duk da haka gwamnati na bakin kokarin maganin wannan matsala”

“Muna da kwarin gwiwar cewa, zuwa watan Disamba wannan kasa za ta rinka fitar da tataccen mai wanda ya hada da namu da za mu tace da kuma na kamfanin Dangote.” (Garba Abdullahi Bagwai)