logo

HAUSA

Jami’in Zambiya ya yabawa Sin bisa shirin horo kan harkokin jagoranci

2024-07-18 10:18:40 CMG Hausa

A jiya Laraba ne Elisha Matambo, babban jami'in gwamnatin kasar Zambiya ya yabawa kasar Sin bisa bayar da horo mai zurfi a fannin inganta harkokin jagoranci da tsare-tsare na sassan tattalin arziki ga manyan jami'an gwamnatin kasar Zambiya.

Elisha Matambo, wanda shi ne ministan lardin Copperbelt, kuma daya daga cikin ministoci da sakatarorin dindindin da aka baiwa wannan horo kwanan nan a kasar Sin, ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da shirya shirin.

Ya ce jami’an za su yi amfani da dimbin ilimin da suka samu a lokacin horaswar domin inganta gudanar da ayyuka a ma’aikatu da larduna daban-daban na gwamnati.

A cewar jami’in a sakonsa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, “Mun yi farin ciki da cewa, horo mai zurfi da muka samu a kasar Sin yana daidai da digiri na biyu a fannin jagoranci da samar da arziki wanda a halin yanzu muke yi a nan kasar Zambiya, kuma za a yaye mu nan ba da jimawa ba.” (Yahaya)