Najeriya na asarar dala biliyan 9 a duk shekara daga ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa izini ba
2024-07-16 11:14:24 CMG Hausa
Kwamitin majalissar wakilan Najeriya a kan sha’anin albarkatun kasa ya sanar da cewa, Najeriya na asarar a kalla dala biliyan 9 a duk shekara daga ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa izinin hukuma ba.
Shugaban kwamiti Hon Jonathan Gbefwi ne ya tabbatar da hakan ranar Litinin 15 ga wata yayin zaman bincike da kwamitin ya gudanar a birnin Abuja, inda ya ce, kudin kawai da yake shiga aljihun gwamnati ba ya wuce kaso 3 na harajin da wasu kalilan din kamfanonin hakar ma’adanai dake da lasisi ke biya.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa, majalissar dokokin ta kasa ta damu matuka a game da irin wannan asara da gwamnati ke yi.
A yayin zaman na jiya dai, kwamitin ya gayyato babban hafsan tsaron kasar Janaral Christopher Musa wanda ya sami wakilcin Air Vice Marshal Nnaemeka Ilo wanda ya shaidawa ’yan kwamitin cewa ya zuwa yanzu dakarun sojin kasar sun samu nasarar kame mutane 387 da suke da alaka da masu aikin hakar ma’adanan ta haramtacciyar hanya.
Sai dai ya ce aikin dakile ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa izini ba, aiki ne da yake bukatar raba shi ga dukkan bangarorin gwamnati.
“Abun tambaya a nan wace rawa jihohi da kananan hukumomi za su taka wajen yaki da hakar ma’adanai ba bisa izini ba? Ina ganin cewa da yawa an dora alhakin wannan yaki kawai kan gwamnatin tarayya alhalin sauran matakan gwamnatin biyu suna da rawar da za su taka sosai.” (Garba Abdullahi Bagwai)