logo

HAUSA

An kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan tsarin lura da wadatar kasa da abinci a tarayyar Najeriya

2024-07-14 16:53:29 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin shugaban kasa da zai lura da tsarin samar da abinci da zummar kawar da yunwa a tsakanin al’umma.

A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da kwamitin ranar Jumma’a 12 ga wata a fadar shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce dabarar samar da kwamitin daya ne daga cikin kokarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kassara tasirin yunwa da tsadar rayuwa a tsakanin ‘yan Najeriya ta hanyar daidaita farashin kayan abinci da aiwatar da tsarin noma irin na zamani.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Sanata Kashim Shettima ya ce a zahirin gaskiya Najeriya na tinkarar mummunan yanayin karancin abinci, amma kuma ba da jimawa ba wannan yanayi zai zama tarihi, ta hanyar sake inganta tsarin noma, samar da ingantaccen iri da kuma takin zamani.

Da yake zantawa da manema labarai, ministan gona da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya ce, kwamitin zai kasance ne karkashin mataimakin shugaban kasa, kuma yana da wakilci daga dukkan matakan gwamnati uku, kama daga kananan hukumomi, jihohi da kuma tarayya, kuma kwamitin zai rinka bayar da rahotonsa ne ga kwamitin lura da cigaban tattalin arzikin kasa wanda yake karkashin jagoranci Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Shi kuwa gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda yana daya daga cikin mambobin kwamitin cewa yake,

“Wannan kwamiti zai duba yiwuwar saka jari a fannin kasuwancin noman abinici ta hanyar hada kai da bangarori masu zaman kansu domin samun damar noma kayan amfanin gona masu yawan gaske, kuma ina da yakinin cewar wannan kwamiti zai yi aikin da ya kamata domin cimma wannan buri”.(Garba Abdullahi Bagwai)