UNECA: Akwai bukatar aiki tukuru kafin cimma moriyar karuwar yawan al’umma a nahiyar Afirka
2024-07-14 16:48:31 CMG Hausa
Wani rahoto na hukumar raya tattalin arzikin nahiyar Afirka ta MDD ko UNECA, ya ce yayin da adadin al’ummun nahiyar Afirka suka haura biliyan 1.5, kuma damar cin gajiya daga yawan al’ummar nahiyar ke karuwa, akwai bukatar aiwatar da managartan manufofi, da jiran lokacin cin gajiyar hakan.
Cikin rahoton, kwararru a fannin nazarin zamantakewar al’umma na UNECA, sun ce nahiyar Afirka ta zama cibiyar karuwar al’ummar duniya, inda yawan jama’arta suka karu daga miliyan 283 a shekarar 1960 zuwa sama da biliyan 1.5 a shekarar nan ta 2024, karuwar da ta kai sama da ninki 5 ya zuwa yanzu.
Kaza lika rahoton na UNECA, ya nuna kyakkyawan fatan cin gajiya daga sauyin yanayin yawan al’ummar nahiyar, da ma karuwar jama’a nan zuwa tsakiyar wannan karni. To sai dai kuma rahoton ya aza ayar tambaya, game da matakan da ya dace kasashen Afirka su dauka, domin daidaita zangon shekarun da za su bayar da cikakkiyar damar cin gajiyar wannan sauyi, da ma irin yanayi da ya dace shekarun ‘yan nahiyar su kasance, don ingiza bunkasar tattalin arzikin nahiyar.
Kwararrun na UNECA, sun ce wadannan muhimman tambayoyi ne da ya kamata a yi la’akari da su, duba da cewa cimma gajiya daga yawan al’umma, ba abu ne dake da tabbashi maras sharadi ba. Maimakon hakan, irin kwazon aiwatar da manufofi na gari da kasashen nahiyar suka yi, da karfafa hukumomi masu zartaswa, su ne za su kai ga haifar da nasarar da ake fata. (Saminu Alhassan)