logo

HAUSA

An kaddamar da wakilan kwamitin tsaro kan batun aikin kidayar jama`a mai zuwa a Nijeriya

2024-07-13 16:49:43 CMG Hausa

Mashawarcin shugaban Nijeriya kan al`amuran tsaro Alh. Nuhu Ribadu ya kaddamar da kwamiti mai wakilai 25 da zai  lura da sha`anin tsaro da kayayyakin aiki a lokacin aikin kidayar jama`a da ta gidaje da za a gudanar a kasar cikin wannan shekara.

Ya kaddamar da `yan kwamitin ne a farkon wannan mako a birnin Abuja, wanda suka kunshi Sojoji da `yan sanda da jami`an tsaron farin kaya da wakilan ma`aikatun gwamnati da kungiyoyi da kuma wakilcin babban bankin kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Yayin bikin kaddamar da `yan kwamitin, Alhaji Nuhu Ribadu ya jaddada bukatar samun sahihin kididdigar al`umma wadda za ta taimakawa manufofin kasa wajen tsara ayyukan cigaba.

Ya ce gwamnati ta nuna damuwa sosai wajen samun nasarar aikin kidayar, inda ya ce samar da kwamitin daya ne daga cikin matakan ganin an gudanar da aikin kidayar cikin kwanciyar hankali tare da kare ma`aikatan hukumar daga duk wata barazana yayin da suke gudanar da rabon kayan aiki.

Ya kuma tabbatar da cewa za a kafa irin wannan kwamiti a matakan jihohin da kananan hukumomin kasar.(Garba Abdullahi Bagwai)