Xi Jinping ya mika tutar girmamawa ga wata rundunar soja ta kasar Sin
2024-07-09 20:49:06 CMG
Xi Jinping, shugaban hukumar koli ta rundunar sojin kasar Sin, ya mika tutar girmamawa ga wata runduna ta rundunar sojin ‘yantar da al’ummar kasar Sin wato PLA, wadda aka ba ta lambar girmamawa ta rundunar soja mai sarrafa motocin yaki masu harba rokoki dake zaman abun koyi, wato "Model Rocket Artillery Company".
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar, ya mika tutar girmamawar ce yayin wani biki da hukumar koli ta sojin kasar ta yi a yau Talata a birnin Beijing.
Haka zalika a yau din, shugaban ya mika takardar umarnin karin girma ga wani hafsan soji zuwa mukamin janar, wanda shi ne mukami mafi girma ga sojojin dake bakin aiki a kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)