An kaddamar da aikin gyaran hanya a DRC
2024-07-04 11:13:46 CMG Hausa
A jiya Laraba ne aka gudanar da bikin kaddamar da aikin gyaran wata hanya a birnin Kananga, babban birnin lardin Kasai na tsakiya na jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC).
Karamin ministan kula da samar da ababen more rayuwa da ayyukan jama’a na DRC Alexi Gisaro Muvuni, da kansa ya tuka motar gyaran hanya domin kaddamar da bikin gyara da zamanantar da hanyar ta lardin Kasai na tsakiya.
Ya ce, bangaren kasar Sin ya karfafa hangen nesa na DRC wajen aikin hada hanyoyi da juna tare da "samar da kudade cikin aminci" da dabaru masu inganci.
Babban daraktan kamfanin samar da ababen more rayuwa na kasar Sin da Congo dake wakiltar bangaren kasar Sin a hadin gwiwar, Pang Long ya bayyana cewa, aikin da ke da tsawon kusan kilomita 230, wanda ya hada Kananga da Kalamba Mbuji, dake kan iyaka da kasar Angola, ana sa ran zai saukaka harkokin sufuri da kasuwanci kan iyakoki. (Yahaya)