Masu bayyana ra’ayi sun amince ruhin SCO ne sabon salon raya huldar kasa da kasa
2024-07-03 10:09:21 CMG Hausa
Yanzu haka hankulan duniya sun karkata ga kungiyar hadin gwiwar Shanghai ko SCO, wadda a matsayinta na kungiyar hadin gwiwa ta kasashe mafiya girma da yawan al’umma a duniya, shugabannin kasashe mambobinta suka hallara a kasar Kazakhstan, domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da ci gaban shiyyarsu.
Wani sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, masu bayyana ra’ayi na da imanin cewa, bayan shekaru sama da 20 na samun ci gaba, kungiyar SCO ta zamo garkuwar tsaro, kuma gadar hadin gwiwa, kana kafar yaukaka abota, kana wani babban karfi na gina shiyyar.
Kaso 82.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na fatan kungiyar SCO za ta zamo kakaki ga kasashe masu tasowa, kana za ta yayata kafuwar tsarin gudanar da harkokin duniya bisa daidaito da sanin ya kamata.
Kasancewar tsaro tushen ci gaba, a matsayinta na mambar kungiyar ta SCO, shawarar wanzar da tsaro a duniya da kasar Sin ta gabatar ta yi daidai da manufar tabbatar da tsaro ta SCO, wanda masu bayyana ra’ayin daga sassan duniya daban daban suka tabbatar da hakan. Cikin masu bayyana hakan, kaso 91.2 bisa dari sun amince cewa, ana iya warware bambance-bambance, da rashin jituwa tsakanin kasashe ne kadai ta hanyar tattaunawa da gudanar da shawarwari, maimakon kakaba takunkumai da yankewa wasu sassa hukunci na radin kai.
Kaza lika, kaso 94.8 bisa dari sun amince tunanin yakin cacar baka, ba abun da zai haifar sai koma-baya ga manufar wanzar da zaman lafiya ta duniya, da danniya, da siyasar nuna karfin tuwo, matakan da kuma za su jefa zaman lafiyar duniya cikin hadari, yayin da fito-na-fito tsakanin kananan rukunoni zai dada fadada kalubalolin tsaro.
Kafar CGTN ta kasar Sin ce ta fitar da sakamakon kuri’un na jin ra’ayin jama’a ta harsunan Turanci, da Faransanci, da Larabci, da harsunan Sifaniya da Rasha, bayan kada kuri’un mutane 13,527 cikin sa’o’i 24. (Saminu Alhassan)