A kalla mutane 18 sun rasu sakamakon hare haren kunar bakin wake a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya
2024-06-30 19:55:28 CMG Hausa
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, ta ce an samu aukuwar hare haren kunar bakin wake 3 a jiya Asabar a garin Gwoza na jihar ta Borno, lamarin da ya haddasa rasuwar a kalla mutane 18 tare da jikkata wasu 40, ciki har da 19 dake cikin mawuyacin halin jinya.
Hukumar ta wallafa a shafin ta na sada zumunta cewa, wasu ‘yan kunar bakin wake sun tada ababen fashewa a wurin wani bikin aure, da wani asibiti, da wani wurin taron jana’iza.
Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da hare haren. (Saminu Alhassan)