Za a wallafa makalar Xi game da manufofi da ayyukan JKS a sabuwar tafiya ta sabon zamani a Quishi
2024-06-30 20:12:05 CMG Hausa
A gobe Litinin ne JKS ke cika shekaru 103 da kafuwa. Kuma albarkacin ranar za a wallafa makalar babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, game da ayyuka da manufofin JKS a sabuwar tafiya ta sabon zamani, a mujallar Quishi wadda ke matsayin muhimmiyar mujallar kwamitin kolin JKS.
A daya bangaren kuma, a yau Lahadi, ofishin tsare tsare na kwamitin kolin JKS, ya fitar da wani rahoto mai kunshe da alkaluman dake nuna cewa, ma’aikata da manoma ne mafiya yawa cikin mambobin JKS, inda adadin su ya kai kaso 33 bisa dari na jimillar mambobin jam’iyyar. (Saminu Alhassan)