Mutane 53 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a Najeriya
2024-06-30 14:45:52 CMG Hausa
Hukumar dakile yaduwar cututtuka a tarayyar Najeriya ta ce ta samu rahoton bullar cutar kwalara har 1,528 a wasu jahohi 31 dake kasar, inda jihar legos ke kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da cutar.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a mako jiya a birnin Abuja game da matsayin annobar, darakta janaral na hukumar Dr. Jide Idris ya ce mutane 53 ne suka mutu sakamakon cutar da aka danganta ta da shan ruwan sama da jama'a ke tara da kuma rashin ingancin muhalli.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Darakta janaral din yace an samu kididdigar mutanen da suka mutu ne a ranar 24 ga watan juni, kuma annobar ta shafi kananan yara da magidanta ne.
Ya alakanta barkewar cutar sakamakon saukar ruwan sama, inda ya tabbatar da cewa a bisa nazarin da kwararru a fannin kiwon lafiya suka gudanar a mako jiyan, sun bayyana cewa Najeriya tana kan gwadaben fuskantar karuwar yaduwar cutar, ko da yake hukumar tare da ma`aikatar lafiya ta tarayyar sun dauki managartan matakan dakile cigaba da yaduwar cutar a kasa baki daya.
Tuni da gwamnatocin jahohi musamman wadanda cutar ba ta shafa ba suka dukufa wajen daukar matakan riga-kafin yaduwar cutar.
Ko a hirar daya gudanar da manema labarai a ranar asabar 29 ga wata kwamashinan lafiya na jihar Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf ya ce.
"Muna yin iyakacin bakin kokarin mu, kuma muna fatan Allah zai kare jihar Kano ba ta kamu da wannan annoba ba, amma kamar case daya ko biyu na cutar kamar yadda aka saba samu in sha Allahu wannan ba zai zama matsala ba, a yanzu dai mun tanadi asibitin Zana wato IDH saboda haka idan muka samu rahoton bullar cutar to za a sanar damu kuma zamu bayar da shawarar cewa a kai mutum wuri kaza." (Garba Abdullahi Bagwai)