logo

HAUSA

Gwamnan yankin Menaka ya yi bitar ayyukan jin kai tare da kungiyoyin jin kai dake kasar Mali

2024-06-30 14:48:46 CMG Hausa

 

Gwamnan yankin Menaka a kasar Mali, manjo kanal Amadou Camara ya gana a ranar jiya Asabar 29 ga watan Junin shekarar 2024 da masu ruwa da tsaki na kungiyoyin jin kai dake cikin yankinsa, domin yin bitar ayyukan da suke yi na ci gaban al’umomi masu rauni dake wannan yankin kasar Mali.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ita dai wannan ganawa na cikin tsarin gabatar da rahoto na lokaci-lokaci na tawagogin jin kai da ke yankin Menaka. A cewar gwamnan wannan yanki, abubuwan da aka lura da su na nuna karara cewa taimakon da ake yi zuwa ga al’umomi da ke fama da karancin abinci a kai a kai bai kai matakin da ake bukata ba.

Bisa wadannan dalilai ne, kamar yadda dokokin kasa suka tanada, da halin siyasa na yanzu na jamhuriyyar kasar Mali, yana da muhimmanci da aka kafa wani tsarin hadin gwiwa na gabatar da rahotanni na lokaci zuwa lokaci bisa la’akari da dukkan ayyukan da ake gudanarwa, in ji gwamnan yankin Menaka, kafin ya isar da godiyarsa ga dukkan masu ruwa da tsaki, musamman ma ga ma’aikatar daidaita harkokin jin kai ta MDD, OCHA bisa ga tallafinta mai ma’ana da tasiri, daga na mataki daban daban da ba su taba kawo wata matsala ba har zuwa yanzu, in ji manjo kanal Amadou Camara, gwamnan yankin Menaka.

A nasu bangare, masu ruwa da tsaki na kungiyoyi da tawagogin jin kai da ke aiki a kasar Mali, sun jadaddawa gwamnan Menaka na ci gaba da taimakawa al’umomin kasar Mali, musamman ma na Menaka, ta yadda ’yan kasar Mali za su ci moriyar ayyukan jin kai, haka ma da kokarin da suka yi wajen kawo ci gbaba mai dorewa tare da tabbatar da zaman lafiya da zaman jituwa.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.