logo

HAUSA

Kungiyar gwamnonin Najeriya za ta ci gaba da kokarin ganin an samar da matsayar karshe na sabon tsarin albashi ga ma’aikata

2024-06-28 09:24:02 CMG Hausa

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce tana bakin kokari wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samun daidaiton bai daya kan batun sabon tsarin mafi kankantar albashi ga ma’aikatan kasar.

Kungiyar ta tabbatar da hakan ne jiya Alhamis 27 ga wata yayin wani taro da gwamnonin suka gudanar a birnin Abuja, inda suka tabbatarwa ’yan Najeriya cewa tattaunawar da ake yi yanzu haka da gwamnati da kungiyar kodago da kuma shugabannin kamfanonin masu zaman kansu za ta haifar da kyakkyawan sakamako.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan fitowa daga taron na jiya, gwamnan jihar Zamfara Alhaji Dauda Lawan ya ce, a karshen tattaunawar da ake yi ne kawai za a iya fitar da shawara ta karshe kan batun albashin ma’aikatan wanda za a aiwatar a dukkan matakai na gwamanti.

“Gwamnoni na ci gaba da tuntuba, saboda haka mai yiwuwa ne zuwa yau din nan Juma‘’a inda mun sake zama za a iya jin sakamako.”

Ha’ila yau taron kungiyar gwamnonin ya tattauna a kan wasu batutuwa na daban da suka shafi kasa wadanda suka kushi manufofin kasafin kudi da kuma sauye-sauyen da ake yi a kan batun haraji. (Garba Abdullahi Bagwai)