logo

HAUSA

Xi: Sin ta fi mai da hankali ga harkokin diplomasiyyarta da Vietnam tsakanin kasashe makwabtanta

2024-06-26 21:06:15 CMG Hausa

Da yammacin yau Laraba 26 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan kasar Vietnam Phạm Minh Chính, wanda ya zo kasar Sin domin halartar taron dandalin tattaunawa na Davos na lokacin zafi.

A yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta fi mai da hankali ga harkokin diplomasiyyarta da Vietnam tsakanin kasashe makwabtanta, kuma tana nuna goyon baya ga Vietnam wajen bin hanyar raya kasa irin ta gurguzu mai dacewa da halinta, kana Sin tana fatan Vietnam za ta kiyaye raya kyakkyawar makomar Sin da Vietnam, bisa manufofi shida, wato kara yin imani da juna kan siyasa, da kara yin hadin gwiwar kiyaye tsaro, da fadada hadin gwiwarsu, da kara sada zumunta a tsakaninsu, da yin hadin gwiwa kan harkokin cudanyar bangarori daban daban, da kuma daidaita matsaloli yadda ya kamata.

Har ila yau, kamata ya yi kasashen biyu su kara bunkasa mu’amala da juna, da zurfafa hadin gwiwarsu, da yin kokari wajen zamanantar da kasa, don samar da gudummawar shimfida zaman lafiya, da karko, da samun bunkasuwa, da wadata a duniya baki daya. (Zainab Zhang)