Jamhuriyar Nijar: Harin da aka kai rundunar soja ya haddasa asarar rayuka
2024-06-26 14:31:14 CMG Hausa
Ma'aikatar tsaron kasar Jamhuriyar Nijar ta sanar a ranar 25 ga wata cewa, wasu 'yan ta'adda sun kai hari kan rundunar sojan kasar, a wani kauyen dake yankin Tillaberi, da safiyar ranar Talata bisa agogon wurin. Lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji 20 da farar hula 1, yayin da sauran sojoji 9 suka jikkata.
Ban da haka, an ce akwai motoci 2 na bangaren soja da suka lalace sakamakon harin. Sai dai yayin da sojojin ke kokarin mayar da martani ga harin da aka kai musu, sun kashe 'yan ta'adda fiye da goma. Yanzu haka, bangaren sojan kasar na girke jiragen saman yaki da karin sojoji masu ba da taimako, a kokarin cafke sauran 'yan ta'addan da suke da alhakin kaddamar da harin. (Bello Wang)