Tsoffin shugabannin kasar Benin Nicephore Soglo da Boni Yayi sun iso birnin Yamai a ranar jiya da yamma
2024-06-25 13:35:59 CMG Hausa
A jamhuriyyar Nijar, kuma tsoffin shugabannin kasar Benin da suka hada da Thomas Yayi Boni da Nicephore Soglo suka kai ziyarar aiki a birnin Yamai a ranar jiya Litinin 24 ga watan Junin shekarar 2024 da yamma bisa ga kokarin daidaita rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Makasudin wannan rangadi na manyan jami’an kasar Benin a Yamai, babban birnin kasar Nijar shi ne na neman rage sabanin dake kasashen Benin da Nijar. Kuma mataki ne da tsoffin shugabannin kasar Benin suka dauka bisa niyyar kansu.
Daga saukarsu a filin jiragen sama na kasa da kasa na Hamani Diori dake birnin Yamai, manyan jami’an biyu sun samu tarbo daga ministan cikin gida janar Mohamed Toumba tare da rakiyar dokta Soumana Boubacar, darektan fadar shugaban kasa, Abdourahamane Tiani.
A maganarsu ta farko, Nicephore Soglo da Yayi Boni sun bayyana cewa, sun zo Yamai, bisa niyyasu domin neman bakin zaren rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Julin shekarar 2023.
Inda suka sun kara bayyana cewa, wannan ziyara tasu na da manufar maido da kyakkyawar dangantaka tsakanin Nijar da Benin, dangantakar da ta samu asili tun fil’azal.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar