Sin ta kalubalanci Japan da ta daina tada zaune tsaye kan batun tekun kudancin Sin
2024-06-21 13:46:32 CMG Hausa
Mai magana da yawun ofishin jakadancin Sin dake kasar Japan ya bayyana cewa, kwanan baya, Japan ta sake yin sakin baki kan batun tekun kudancin Sin, inda ta zargi kasar Sin ba gaira ba dalili, ofishin na matukar rashin jin dadi game da hakan.
Wannan jami’in ya nanata cewa, batun sashen tudun ruwa na Ren’ai babu wani shakku a cikinsa. Kasar Philippines ta yi biris da kashedin da Sin take yi mata, ta samarwa jirgin ruwan yaki da ta jibge a tudun ruwa na Ren’ai tallafi da nufin mamaye wannan wuri na kasar Sin. Matakan da ’yan sandan tekun kasar Sin suka dauka sun dace da doka da oda, kuma sun bayyana kwarewarsu na kiyaye sararin tekun kasar. Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace kan duk wani matakin takara da kasar Philippines za ta dauka, don kiyaye muradun ikon mulkin kasar.
Jami’in ya kara da cewa, ba ruwan Japan da batun tekun kudancin Sin ko kadan, ba ta isa ta tsoma baki cikin batun dake shafar Sin da Philippines ba. Hadin kan da Japan take yi da Amurka da Philippines, kar ya keta ikon Sin na mallakar filaye da sararin teku, bai kamata Japan ta zama inuwa guda tare da Philippines kan haramtaccen matsayin da kasar Philippines ke dauka. (Amina Xu)