Nijar na karbar cikin kasarta fiye da ’yan gudun hijira 411,268 na kasashe daban daban
2024-06-21 09:14:23 CMG Hausa
A ranar jiya 20 ga watan Junin shekarar 2024, kasar Nijar ta bikin ranar kasa da kasa ta ’yan gudun hijira karo na 23 bisa taken zumunci tare da ’yan gudun hijira tare da sauran kasashen duniya. A albarkacin wannan rana, ministan cikin gida, birgadiye-janar Mohamed Toumba, ya yaba da kokari da juriyar wadannan mutane da aka tilastawa barin kasashensu, da muhallinsu domin guje ma yake-yake ko zalunci.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Kamar yadda taken wannan shekara ya nuna zumunci tare da ’yan gudun hijira, na bayyana nuna damuwa da nuna goyon baya, da nuna abokantaka zuwa ga miliyoyin ’yan gudun hijira a duniya, dake ci gaba da bayyana fatansu na ganin daidaituwar kome, domin wata rana su koma cikin kasashensu na asali da sake maido da zaman rayuwarsu.
A cikin jawabinsa, minista Mohamed Toumba ya yi bayani cewa, ’yan gudun hijira na kasancewa babban nauyi ga kasashen dake karbarsu, inda ya kara da cewa, al’ummar Nijar na ci gaba da daukar nauyin da ya rataya kan wuyanta, da kuma ci gaba da karbar ’yan gudun hijira, tare da girmama su da ba su darajarsu.
Haka kuma, ministan cikin gida ya yi amfani da wannan dama, domin nuna niyyar gwamnnatin Nijar kan girmama dokokin kasa da kasa da wasu ka’idodi na shiyya-shiyya dake nasaba da kare mutanen da suka yi gudun tashe-tashen hankali, da take ’yancinsu na dan Adam.
A halin yanzu, kasar Nijar na karbar ’yan gudun hijira kimanin dubu 411 da dari 268 na mutanen da suka fito daga kasashe daban daban, dake samun kariya da kulawa a kasar Nijar.
Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.