Sallar Layya : shugaban CNSP ya halarci sallar Idi a babban masallacin Kaddhafi da ke birnin Yamai
2024-06-17 14:13:00 CMG Hausa
Kasar Nijar kamar wasu sauran kasashen musulmi na duniya, ta yi bikin sallar Layya ko Aid El Adha a ranar jiya Lahadi 16 ga watan Junin shekarar 2024. Shugaban kasa kuma shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, Abdourahamane Tiani ya halarci sallar Idin da ta gudana a babban masallacin Kadadhafi da ke birnin Yamai.
Daga birnin Yamai din abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.