Tawagar AU ta ce janyewar dakaru ba zai bar gibin tsaro a Somaliya ba
2024-06-17 09:28:46 CMG Hausa
Babban wakilin kungiyar tarayyar Afirka AU a kasar Somaliya, ya tabbatar wa 'yan Somaliya cewa, janyewar sojoji daga kasar ba zai haifar da wani yanayi na gibi ga tsaron kasar ba.
Wakilin kungiyar AU na musamman kan kasar Somaliya Mohamed El-Amine Souef, ya ce kungiyar ta kasashen Afirka ba za ta yi watsi da Somaliya ba, duk da shirin da tawagar wanzar da zaman lafiya ta AU a Somaliya ko ATMIS ke yi na janye karin dakaru 4,000 a karshen watan Yuni.
"Duk da rage yawan dakarun ATMIS, za mu tabbatar da cewa babu wani gibi na tsaro," a cewar Souef bayan wata ziyarar kwanaki biyu da ya kai birnin Jowhar da ke kudu maso tsakiyar kasar Somalia, a cikin wata sanarwa da aka fitar a Mogadishu babban birnin Somalia a daren Asabar.
Ya ce za a daidaita tsarin mika ikon kula da tsaro tsakanin jihohin tarayyar kasar (FMS), da gwamnatin Somaliya, da kuma abokan huldar kasa da kasa.
A yayin ziyarar, Souef ya yaba wa dakarun Burundi bisa kokarin da suke yi na tunkara da fatattakar kungiyar al-Shabab, inda ya bukace su da su kasance a ankare da hada kai da jami'an tsaron Somaliya da al'ummar yankin. Bisa kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2710 na shekarar 2023, an umarci ATMIS da ta janye dakaru 4,000 a mataki na uku na janye sojojinta, sannan kuma a maye gurbinsu da jami'an tsaron Somaliya. (Yahaya)