logo

HAUSA

Tsoffin shugabannin Najeriya suna fatan kasarsu ta dogara da kanta wajen samar da abinci

2024-06-17 14:05:41 CMG Hausa

Tsoffin shugabannin tarayyar Najeriya sun yi kira ga al'ummar kasar da su goyi bayan duk wani shiri da zai kai ga kasar tana dogara da kanta ta fuskar samar da abinci da kyautata sha'anin tsaro.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Janral Abdulsalami Abubakar ne suka yi kiran a sakonsu na salla ga al'ummar kasar jim kadan da kammala Sallar Idi jiya Lahadi 16 ga wata a garuruwansu daban daban, sun ce sai an fi karfin abinci tsaro zai inganta.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.