logo

HAUSA

Yawan kudin jigilar hajoji ta bangaren ciniki a Sin a shekarar 2023 ya kai fiye da dala triliyan 17

2024-06-17 10:46:56 CMG Hausa

 

A gun taron tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayyar Sin da ketare na shekarar 2024 da aka yi a birnin Langfang na kasar Sin a jiya Lahadi, an gabatar da “rahoton bunkasuwar aikin jigilar hajoji ta bangaren ciniki a Sin a shekarar 2023”, inda ya nuna cewa, yawan kudi a wannan fanni ya kai kudin Sin Yuan triliyan 126.1, kwatankwacin dalar Amurka fiye da triliyan 17, wanda ya karu da kashi 5% bisa na makamancin lokaci na bara.

Rahoton kuma ya nuna cewa, a halin yanzu aikin jigilar sufuri a bangaren ciniki na samun bunkasuwa a bangarori 6, wato da farko dai, aikin jigilar sarin kayayyaki ya habaka zuwa ba da hidima ga tsarin samar da kayayyaki. Na biyu kuma, an gaggauta yiwa aikin jigilar hajojin da ba na sari ba kwaskwarima. Na uku shi ne aikin jigilar kayayyaki mai bukatar na’urar sanyi ya samu kyautatuwa. Kana, aikin jigilar kayayyakin abinci da otel-otel da dakunan sayar da abinci suke bukata na samun saurin bunkasuwa. Na biyar kuwa, aikin jigilar kayayyakin shige da fice na samun bunkasuwa mai dorewa. Daga karshe dai, mizanin jigilar kaya ba tare da gurbata muhalli ya kyautatu matuka.

Ban da wannan kuma, rahoton ya yi hasashe kan bunkasuwar aikin jigilar hojoji a shekarar 2024 da muke ciki. (Amina Xu)