logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga da dama

2024-06-14 14:02:26 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar a ranar Alhamis cewa, an kashe ‘yan bindiga da dama ciki har da wani gawurtaccen shugaban ‘yan bindiga a wani samame da sojojin Najeriya suka kai a jihar ta Kaduna da ke arewacin kasar. 

Sojojin sun kai samamen ne a maboyar ‘yan bindiga a dajin Idasu da ke tsakanin karamar hukumar Giwa da Sabuwa, inda suka yi artabu da ‘yan ta’adda da dama, a cewar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na Kaduna.

“Gawurtaccen dan ta’adda wato Buharin Yadi, daya daga cikin jagororin ‘yan bindiga da suke aikata ta’addanci a arewacin Najeriya a cikin shekaru goma da suka gabata, ya gamu da ajalinsa a hannun jami’an tsaro”, a cewar sanarwar, inda ta ce sojojin sun yi ruwan wuta a kan ‘yan bindiga kuma suka kashe a kalla 36 daga cikinsu. (Yahaya)