logo

HAUSA

Sojoji 9 da wasu jami’an tsaro 7 na Najeriya ne ’yan bindiga suka hallaka a Zamfara

2024-06-14 09:20:42 CMG Hausa

 

Hedikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa, sojoji 9 ne tare da wasu jami’an tsaro 7 ’yan bindiga suka kashe a farkon wannan watan na Yuni a lokacin da suke tsaka da yaki da ayyukan ’yan ta’adda da kuma masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara.

Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron ta kasa Major Janaral Edward Buba ne ya tabbatar da hakan jiya Alhamis 13 ga watan lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan zargin da gwamnan jihar Zamfara ya yi nacewa gazawar jami’an tsaro shi ne dalilin da ya sanya gwamnati kirkiro da jami’an tsaron sa kai a jihar domin su ci gaba da kare al’umma daga farmakin ’yan ta’adda.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  

Major janaral Edward Buba ya bayyana wannan zargi da cewa, ko kadan ba haka yake ba, inda ya ce sojoji suna bakin kokarinsu sosai wajen maganin ayyukan  ta’addanci a jihar wadda ta zama tamkar matattarar ’yan ta’adda a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.

Ya ce, a kan wannan aiki ne ma wasu daga cikin jami’an soji 9 da ma’aikatan wasu hukumomin tsaro su 7 suka rasa rayukansu a farkon wannan wata na Yuni.

“Jihar Zamfara ba ta da ingantacce tsarin tsaro na cikin gida da zai baiwa dakarun soji damar gudanar da ayyukansu, za ka ga cewa wasu jihohin da ba su kai jihar Zamfara matsalolin tsaro ba amma suna da tsari mai kyau da yake taimakon dakarun tsaro tafiyar da ayyukansu.”

Ya jaddada cewa samun nasarar yaki da ’yan ta’adda ba tare da samun hadin kan al’ummar gari ba abu ne mai wahalar gaske haka zalika.

“Samun nasarar yaki da ’yan ta’adda ba tare da goyon bayan gwamna ba aiki ne babba mai wahalar tabbatuwa.” (Garba Abdullahi Bagwai)