logo

HAUSA

Ciniki tsakanin Sin da kasashen waje na samun bunkasuwa yadda ya kamata

2024-06-13 11:37:12 CMG Hausa

 

Alkaluman da kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Mayun bana, darajar cinikin shige da fice na kasar ta kai kudin Sin Yuan triliyan 17.5, kwatankwacin fiye da dalar Amurka biliyan 2413.5, wanda ya karu da 6.3% bisa makamancin lokacin bara. Abin lura shi ne, saurin bunkasuwar cinikin shige da fice a watan Mayu ya kai 8.6%, wanda ya karu da 0.6% bisa na watan Afrilu. Kafofin yada labaran kasashen waje, ciki hadda Reuters sun nuna cewa, cinikin da Sin take yi da kasashen waje na samun ci gaba fiye da hasashen da aka yi, duk da shingayen da Amurka da wasu kasashen Turai suka sanyawa kasar, lamarin dake bayyana cewa, kamfanonin Sin sun cimma nasarar habaka kasuwannin ketare, kana tattalin arzikin kasar Sin na da karfin juriya.

Hakika dai, ba hajoji kawai kasar Sin take sanarwa duniya ba, ta kuma gabatarwa duk duniya sabbin damarmaki da babbar kasuwa. Alkaluma na nuna cewa, a cikin watanni 5 na farkon bana, yawan hajojin da Sin ta shigo da su ya karu da 6.4% bisa na makamancin lokacin a bara, tana kara shigo da kayayyaki masu yawa.

A kwanakin baya, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF da bankin Paris na kasar Faransa da bankin Amurka da sauran hukumomin hada-hadar kudi a duniya, sun kyautata hasashensu kan bunkasar tattalin arzikin Sin zuwa 5%, saboda yadda ciniki ke samun bunkasuwa tsakanin Sin da kasashen ketare. Kafofin yada labarai na duniya da dama sun nuna cewa, a kasar Sin, GDPn mai yawa da kyakkyawan tsare-tsaren masana’antu, da karuwar yawan mutane masu matsakaicin kudin shiga, sun zama abubuwan da masu zuba jari na kasashen waje ba za su yi watsi da su ba, kuma Sin jigo ne mafi girma na ci gaban tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)