logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci kungiyoyin kodagon kasar da su dawo kan teburin sulhu maimakon tafiya yajin aiki

2024-06-03 10:25:31 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira ga kungiyoyin Kodagon kasar da su janye batun tafiya yajin aiki da suka tsara farawa daga yau Litinin, ya fi dacewa su dawo teburin sulhu domin ci gaba da tattaunawa da gwamnatin.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasar Alhaji Mohammed Idris ne ya bukaci hakan yayin wani taron manema labarai ranar Asabar 1 ga wata a birnin Abuja. Ya ce gwamnatin tarayyar tana son warware matsalolin ma’aikata ta hanyar sulhu da tattaunawa bangarori.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan yada labarai na tarayyar Najeriya ya ce, bisa la’akari da yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma dimbin alkawuran ayyukan raya kasa da gwamnati ta daukar wa al’ummar kasar, akwai bukatar kungiyoyin Kodago su dawo domin ci gaba da zama da ’yan kwamitin da gwamnati ta kafa game da batun mafi kankantar albashi.

“Batun kyautata yanayin rayuwar ’yan Najeriya sama da miliyan dari 2 nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati, a sabo da haka shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba wai kawai zai fifita damuwar ma’aikatan gwamnatin tarayya ba ne kadai wanda duka adadinsu bai wuce miliyan daya da dubu dari biyu ba.”

Ministan ya ce, shugaba Tinubu a shirye yake ya kula da jin dadin duk wani dan kasa, amma ba zai taba amincewa da duk wani yunkuri da zai yi sanadiyyar asarar ayyukan wasu ba.

“Ko da kafin ma a fara tattaunawa a kan batun tsarin mafi kankantar albashi, gwamnatin tarayya ta dauki matakai masu yawa domin saukaka wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta, musammam ma ma’aikatan tarayya, daya daga cikin irin wadannan matakai sun hada da garabasar albashi na naira dubu 35 wanda aka tsara za’a shafe watanni shida ana yi, amma kuma daga bisani ma gwamnatin tarayyar ta ce, ma’aikatan za su ci gaba da amfana da shirin har zuwa lokacin da aka kammala zartar da shawara a kan batun sabon tsarin albashin.” (Garba Abdullahi Bagwai)