logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Gombe ta jagoranci taron masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin maganin rikicin manoma da makiyaya

2024-06-01 16:56:46 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Gombe ta ce tana cigaba da samun nasarori masu yawan gaske a kokarin da take yi wajen kawo karshen yawan rigingimun manoma da makiyaya a jihar.

Kwamishinan ayyukan gona na jihar Mr. Barnabas Malle ne ya tabbatar da hakan a garin Gombe  ranar Larabar da ta gabata yayin babban taron masu ruwa da tsaki kan sha`anin noma da kiwo, ya ce babu shakka yanzu akwai fahimta mai kyau tsakanin manoma da makiyayan dake jihar.

Daga tarayyar Najeriya walilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kwamishinan ayyukan gona na jihar ta Gombe ya ce gwamnati tana asara sosai a duk lokacin da aka fuskanci rigingimu tsakanin wadannan bangarori guda biyu.

Ya ce jihar Gombe jiha ce mai arzikin noma da kiwo a tsakanin jihohin dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, a don haka ba zai taba yiwuwa ba a ce gwamanti ta zuba ido a cigaba da samun tsananin adawa tsakanin manoma da makiyaya wadanda dukkanninsu jigo ne ga bunkasuwar harkokin kudaden shigar jihar.

Mr. Barnabas Malle yace kowanne bangare yana da laifin a rikicin manoma da makiyaya, inda ya bayyana cewa bakin makiyaya na shiga gonakin jama`a saboda rashin sanin hanyoyi da wuraren da suka kasance haramun ne a tura dabbobi ciki, yayin da su kuma wasu daga cikin manoma suna yiwa doka karan tsaye wajen cin iyakoki da aka kebe a matsayin hanya da wurin kiwo ga makiyayan dake jihar.

“A doka dai babu batun shigowar bakin makiya, sannan kuma makiyayan da suke a jihar kamata ya yi su ma su kasance a wuri guda ba tare da haura iyakar jihar ba”

A jawabin sa wakilin kungiyar Fulani makiyaya, kuma shugaban kungiyar Miyeeti Allah reshen jihar Gombe Alhaji Modibbo Yahaya kira ya yi ga gwamnati da ta shigo da Fulani makiyaya cikin al`umma ta hanyar baiwa `ya `yan su ilimi tare da horo a kan dabarun kiwon zamani, da kuma na lura da lafiyar dabbobin su, inda ya ce yin haka zai kara rage yawan fitintinun da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya a jahar ta Gombe.(Garba Abdullahi Bagwai)