logo

HAUSA

An kaddamar da kashin farko na layin jirgin kasa da kamfanin Sin ya gina a birnin Abuja

2024-05-31 14:55:04 CMG Hausa

 

An fara amfani da kashin farko na layin jirgin kasa da kamfanin Sin ya gina a birnin Abuja, fadar mulkin kasar Najeriya. Wannan layin jirgin kasa ya kasance irinsa na farko a Abuja da kamfanin Sin ya taimaka wajen ginawa, bayan da aka kyautata rukunin injunan kona makamashi kirar kasar Sin dake cikinsa. Shugaban kasar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettim da sauran manyan jami’an kasar da ma mukadashin jakadan Sin dake Najeriya, Zhang Yi sun halarci bikin da ya gudana a jiya.

A cikin jawabinsa, Bola Tinubu ya gode da muhimmiyar rawar da kamfanin Sin ya taka wajen gina kashin farko na layin jirgin. Ya ce, wannan layi ya kasance tamkar yiwa tsarin zirga-zirgar kasar kwaskwarima da raya tattalin arziki da zaman takewar al’umma, kuma ya kasance alamar dake bayyana ci gaban da kasar ta samu. Ya kuma bayyana niyya da karfin gwamnati na zamanintar da tsarin sufurin jama’a da kawar da cunkoso da samar saukin zirga-zirga. (Amina Xu)