logo

HAUSA

Sudan ta yi watsi da bukatar Amurka ta komawa ga tattaunawar Jedda

2024-05-30 09:56:39 CMG Hausa

Gwamnatin Sudan, ta bayyana rashin amincewarta da kiran Amurka na komawa ga dandalin tattaunawa na Jedda, tsakanin dakarun gwamnatin kasar na SAF da kuma mayakan RSF.

Mataimakin shugaban gwamnatin riko na kasar Sudan Malik Agar, ya ce gayyatar da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi wa shugaban majalisar riko ta kasar, Abdel Fattah Al-Burhan da ya je birnin Jedda domin tattaunawar na kunshe da raini ga Sudan din, kuma abu ne da ba za a amince da shi ba.

Ya bayyana cewa, matakin da ake ciki yanzu ba zai iya jure tsoma bakin wasu bangarorin siyasa dake da wasu ajandun sabanin na kasar ba, yana mai jaddada cewa dole ne a bayar da fifiko ga kawo karshen rikicin da samar da zaman lafiya, kafin a kai ga cimma yarjejeniya ta hanyar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu na kasar ta Sudan.

Tun daga ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2023, Sudan ta fara fama da mummunan rikici tsakanin dakarun SAF da na RSF. Bisa kiyasin ofishin MDD mai kula da ayyukan agajin jin kai, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane 15,550 tare da raba wasu miliyan 8.8 da matsugunansu. (Fa’iza)