logo

HAUSA

Najeriya ta yi bikin cika shekaru 25 a mulkin demokradiya ba tare da yankewa ba

2024-05-30 09:53:06 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun al’ummar kasar wajen bikin cika shekaru 25 ana mulkin demokradiyya ba tare da samun wata matsala ba.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa albarkacin wannan rana yayin zaman hadin gwiwa na majalissun dokokin kasar jiya Laraba 29 ga wata, shugaban ya yabawa zaurinka majalissun biyu bisa juriya da jajircewa wajen dorewar mulkin demokradiyya a kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Shugaban na tarayyar Najeriya wanda ya isa zauren majalissar tare da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima, ya jagoranci rera sabon taken Najeriya da ya sanyawa hannu a kwanakin baya, ya ce babu shakka ’yan majalissar sun cancanci yabo bayan kare muradun demokradiyya da suka yi har na tsawon wadannan shekaru.

Shugaban Bola Ahmed Tinubu wanda ya mika sakon murnarsa ga tsoffi da sabbin abokan nasa da sauran daukacin ’yan Najeriya bisa yadda suka daure wajen biyayya ga dokokin da suke tattare da mulkin siyasa duk kuwa da kalubalen da tsarin ya yi ta tsintar kansa a ciki.

Shugaban ya bayyana ’yan majalissar a matsayin muryar al’ummar kasa, a don haka akwai bukatar su kara hada kansu tare da baiwa bangaren zartarwa goyon bayan da ya kamata.

“Akwai bukatar ku ci gaba da yin aiki tare a junanku wajen gina kasarmu, ba mu da wani zabi, wannan ita ce kasarmu a bar alfaharin mu, babu wata gudummawa daga waje ko kuma wata hukuma ta kasa da kasa ko wani mutum guda da zai taimaka mana, wajibi ne mu mike tsaye wajen neman na kanmu.”

Daga karshen shugaban na Najeriya ya shaidawa ’yan majalissar cewa ba da jimawa ba zai gabatar masu da kwarkwaryar kasafin kudi na cike gibi, inda ya yi fata samun hadin kansu, kamar yadda suka ba shi yayin kasasfin kudin 2024. (Garba Abdullahi Bagwai)