logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da gudummawar motoci da babura ga hukumomin tsaro

2024-05-29 14:08:33 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewacin Najeriya ta kaddamar da bayar da gudummawar motoci da babura ga hukumomin tsaro dake jihar domin su samu kwarin gwiwar yakar ’yan ta’adda da suka addabi wasu sassan jihar.

Gwamnan jihar Sanata Uba Sani ne ya kaddamar da bayar da motoci da baburan jiya Talata 28 ga rundunar ’yan sanda ta jihar da dakarun soji da suke gudanar da aikin tsaro na musamamn a jihar da kuma sauran hukumomin tsaro. Ya ce, gwamnati ta sayo abubuwan hawan ne domin kara kwarin gwiwa ga jami’an tsaro.

Daga tarayyar Najeriya wkailinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Motoci 150 da babura 500 aka rabawa hukumomin tsaro a wannan kwarya-kwaryar bikin da aka gudanar a garin Kaduna wanda kuma ya sami halartar sarakuna da jami’an gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki.

Da yake jawabi, gwamnan na jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya ce, gwamnatinsa ta lura da irin kalubalen da jami’an tsaro a jihar ke cin karo da su a bangaren ababen hawa domin tunkarar ’yan ta’adda da suke boye a wurare masu wahalar shiga a jihar. 

“Nauyi ne da ya rataya a wuyanmu, mu rinka taimakawa hukumomin tsaro wajen samun nasarar gudanarwar ayyukansu, kaddamar da wadannan motoci da babura ga jami’an tsaro ba wai kawai ya tsaya ne kan samar masu da kayan aiki ba, a’a ya nuna kishin da muke da shi na ci gaba da goya masu bayan a ko da yaushe.”

A jawabinsa, babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ya shaidawa gwamnan cewa, rundunar tsaron Najeriya ba za ta taba saurarawa ba a yakin da take yi da duk wani dan ta’adda a kasa baki daya.

“Ina son na mika matukar godiya ta gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Sanata Uba Sani saboda wannan gudummawa ta motoci kirar Hilux guda 150 da babura 500, wannan abu da gwamnan ya yi irinsa muke nema wato taimako na zahiri ba wai kai yawan maganganu ba.” 

Daga karshe ya tabbatarwa gwamnatin jihar ta Kaduna cewa, za a yi amfani da abubuwan hawan bisa dalilai da suka sanya aka bayar da su. (Garba Abdullahi Bagwai)