logo

HAUSA

Jami’in ofishin jakadancin Sin a Zambia ya jinjinawa kakkarfan zumuncin dake tsakanin Sin da Zambia

2024-05-28 10:00:44 CMG Hausa

Jami’in lura da harkokin raya tattalin arziki da cinikayya a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Zambia Liu Guoyu, ya yaba da kakkarfan hadin gwiwa dake wanzuwa tsakanin Sin da kasar Zambia cikin shekaru masu yawa, yana mai fatan ci gaba da yaukakar hakan a nan gaba.

Liu Guoyu, ya yi tsokacin ne yayin bikin kaddamar da aikin daga martabar wata hanyar dake hadewa da asibitin koyarwa na Levy Mwanawasa, a birnin Lusaka, fadar mulkin kasar Zambia, wanda kasar Sin ta samar da kudaden tallafin ginawa.

Cikin tsokacin nasa, jakada Liu ya ce, har kullum kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan Zambia ta fuskar yayata manufar zamanantarwa, da inganta zaman rayuwar al’ummun kasa, da ingiza ci gaba da farfadowar Zambia.

Kungiyar Sinawa dake Zambia ce ta samar da kudaden da za a yi amfani da su wajen sabunta ginin hanyar, wadda tuni aka sauya sunanta zuwa hanyar kawancen Sin da Zambia. Hanyar na kunshe da sassan tafiya a kasa, da fitilu masu amfani da hasken rana da lambu mai kayatarwa.

(Saminu Alhassan)