logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun hallaka a kalla mutane 7 tare da garkuwa da sama da mutane 150 a jihar Naija dake tsakiyar Najeriya

2024-05-28 10:06:23 CMG Hausa

 

Rahotanni daga jihar Naija dake shiyyar tsakiyar Najeriya na cewa, wasu gungun ‘yan bindiga sun farwa kauyen Kuchi dake karamar hukumar Munya na jihar a daren ranar Juma’a, inda suka harbe a kalla mutane 7 ciki har da ‘yan sanda 4.

Majiyoyi daga jihar sun ce, baya ga mutanen da ‘yan bindigar suka hallaka, sun kuma yi awon gaba da karin wasu mutanen sama da 150. (Saminu Alhassan)