logo

HAUSA

Najeriya da Benin sun sha alwashin kyautata harkakokin kasuwancin dake tsakanin su

2024-05-24 11:12:25 CMG Hausa

Najeriya da jamhuriyar Benin sun amince su kara karfafa sha`anin kasuwanci ta amfani da iyakokin dake tsakanin su.

Kasashen biyu sun amince da hakan ne yayin da ministan harkokin kasashen waje na Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya gana da takwaransa na jamhuriyar Benin Mr. Olushegun Adjadi-Bakari a yankin Tsamiya dake iyakar jihar Kebbi da jamhuriyar Benin, yace dukkan kasashen suna mutukar amfana da kasuwancin dake wakana a kan iyakokin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Iyakar Tsamiya dake Najeriya da kuma Anguwar Sule-Wara dake jamhuriyar Benin,su ne iyakokin da suka hade kasashen biyu daga bangaren jihar Kebbi, kuma sun dauki lokaci a rufe.

A jawabinsa ministan harkokin kasashen waje na Najeriya Alhaji Yusuf Tuggar ya ce bayan tattaunawa da shugabannin kasashen biyu suka yi, shugaban tarayyar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin samar da dukkan kayayyakin aikin da suka kamata domin tabbatar da dawo da hada-hada a kan iyakokin.

Ministan ya ce a kan haka ne ya jagoranci tawagar da ta kunshi shugaban hukumar kwastam na Najeriya da gwamnan jihar Kebbi da sauran masu ruwa da tsaki domin ganawa da takwarorinsu na jamhuriyar Benin.

“Zuwan mu wannan waje a wannan rana ci gaba ne daga cikin kokarin da kasashen biyu ke yi karkashin umarnin shugaba Tinubu da takwaransa na Benin Mr Talon na share hawayen ‘yan kasuwa da kuma al`ummomin dake shige da ficen kasuwanci ta amfani da kan iyakar, lamarin da zai kara karfafa harkokin walwala da kuma na tattalin arzikin kasashen biyu”

A jawabinsa ministan harkokin wajen kasar Benin Mr. Olushegun Adjadi-Bakari cewa yake.

“Wannan taro wata babbar dama a gare mu da za mu tattauna yadda za a shawo kan sauran matsalolin da al`ummomin dake zaune a kan iyakoki ke ciki baya ga bunkasa kasuwanci” (Garba Abdullahi Bagwai)