logo

HAUSA

Cadi: Mamahat Deby Itno yayi rantsuwar kama aiki tare da nada Allamaye Halina a matsayin sabon faraminista

2024-05-24 15:49:29 CMG Hausa

A ranar jiya 23 ga watan Mayun shekarar 2024 aka rantsar da Mahamat Idriss Deby Itno, a matsayin shugaban kasar Cadi bayan lashe zaben shugaban kasa da kashi 61 cikin 100.

Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto.

A yayin bikin rantsuwar kama aiki, sabon shugaban Cadi ya yaba da dawowar tsarin demokuradiyya, tare da alkawarin kasancewa shugaban dukkan ‘yan kasar Cadi maza da mata, ba tare da nuna bambanci ba, kasancewa shugaban dukkan masu mabambantan addinai na kasar, da na dukkan al’ummomi masu mabambantan jam’iyyun siyasa.

Jim kadan bayan rantuwar kama aiki, ya nada Allamaye Halina, tsohon jakadan kasar Cadi a kasar Sin, a matsayin sabon faraministan kasar.

An zabe shi  a matsayin shugaban kasa a ranar 6 ga watan Mayu da kashi 61 cikin 100 na kuri’un da aka jefa, lamarin da ya kawo karshen mulkin wucin gadinsa, bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno. (Mamane Ada)