logo

HAUSA

Mukaddashin jakadan Sin a Najeriya ya gana da ministar raya al’adun kasar

2024-05-22 20:41:57 CMG Hausa

Mukaddashin jakadan Sin a Najeriya Zhang Yi, ya gana da ministar ma’aikatar raya al’adun kasar Hannatu Musawa, jiya Talata a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Yayin zantawarsu, sassan biyu sun yi tattauna mai ma’ana game da batutuwan da suka shafi bunkasa matsayin musayar al’adu, da hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya, da karfafa bayar da horo game da adabi, da basirar masu fasahohi, da jami’an raya al’adun sassan biyu.

Zhang Yi, ya bayyana aniyar kasar Sin ta ci gaba da bunkasa sassan hadin gwiwa da Najeriya, ta yadda sakamakon hadin gwiwar cimma moriyar juna tsakanin kasashen biyu zai kara amfanar al’ummun su.

A nata bangare kuwa, Musawa cewa ta yi fatan ta shi ne a nan gaba, sassan biyu za su nunawa juna al’adun su masu ban sha’awa, tare da cin gajiya daga ribar hadin gwiwar su, karkashin ayyukan hadin kai daban daban na raya al’adu.   (Saminu Alhassan)