logo

HAUSA

An bude taron musamman karo na biyu na kungiyar ‘yan majalissun kasashen ECOWAS a Najeriya

2024-05-22 14:13:27 CMG Hausa

Kungiyar ‘yan majalissun kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS ta bayyana shirin samar da kwamitin da zai shawo kan kasashen da suka juyawa kungiyar baya.

Kungiyar ta zartar da wannan shawara ce yayin taronta na musamman karo na biyu da aka bude jiya Talata 21 a birnin Kano dake arewacin Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Da yake jawabi yayin bude taron, mataimakin kakakin majalissar ta ECOWAS Sanata Barau Jibril ya jaddada bukatar sanya bakin ‘yan majalissar a kan duk wani abu da ya shafi shiyyar yammacin Afrika, inda ya ce sun tattauna da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar, gabannin wannan taro matsayin kasashen da suka fice daga kungiyar.

Sanata Barau Jibril wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalissar dattawan Najeriya ya tabbatar da cewa, dukkannin masu ruwa da tsaki dake kungiyar sun nuna bukatar gaggauta wajen daukar matakai da za su hana rabuwar kawuna a cikin kungiyar, bisa la’akari da ficewar kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso wanda babu shakka ficewar tasu za ta haifar karuwar matsalolin tsaro a yankin Sahel.

Mataimakin kakakin majalissar kungiyar ta ECOWAS ya ce a sakamakon haka ne ya gabatar da bukatar nada karamin kwamiti da zai shiga tsakani, kuma ‘yan kwamitin za su yi aiki ne tare da masu ruwa da tsaki da nufin sanya kasashen uku su sauya tunani game da matakin da suka dauka na fita daga cikin kungiyar.

“Wannan taro zai bayar da damar tattaunawa a kan sauran fannonin cigaban kasashen dake cikin kungiyar, musamman ma dai wadanda suke da nasaba da cigaban tattalin arziki da siyasa da kuma tsaro.”

A kan rashin halartar wakilai daga kasar Togo kuwa, wajen wannan taron, sanata Barau Jibril ya ce majalissar kungiyar ta ECOWAS ta nada wakilai da za su je kasar Togo domin jin dalilan da ya sanya wakilan kasar ba su samu halartar taron da aka bude jiya Talata ba.

A ranar juma’a 24 ga wata ne dai za a kammala taron. (Garba Abdullahi Bagwai)