logo

HAUSA

Shugaban wucin gadi na Chadi ya lashe babban zabe

2024-05-17 14:58:38 CMG Hausa

 

Kwamitin kundin tsarin mulkin kasar Chadi ya gabatar da sakamakon zaben shugaban kasa a birnin N'Djamena, fadar mulkin kasar. Inda aka nuna cewa, shugaban wucin gadi na kasar Mahamat Idriss Deby, ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 6 ga watan nan.

Sakamakon ya bayyana cewa, Mahamat Idriss Deby mai shekaru 40 da haihuwa, ya samu kaso 61% na jimillar kuri’un da aka kada, yayin da dan takarar jam’iyyar adawa, kana firaministan wucin gadi Succes Masra, ke biye a matsayi na biyu da kaso 18.54% na jimillar kuri’un zaben.

Bisa alkaluman da kwamitin kundin tsarin mulkin kasar ya gabatar, kaso 75.78% na masu kada kuri’un da suka yi rajista ne suka kada kuri’unsu a yayin babban zaben na kasar Chadi. (Amina Xu)