logo

HAUSA

Kamfanin Huawei ya kaddamar da sayar da kayayyakin samar da wutar sola ga masana’antu a jihar Kano

2024-05-15 09:42:49 CMG Hausa

Kamfanin kere-keren kayayyakin fasaha na kasar Sin Huawei ya kaddamar da sayar da kayayyakin samar da wuta ta amfani da hasken rana ga masana’antu da wuraren kasuwanci da kuma gidaje a jihar Kano dake arewacin Najeriya.

A lokacin da yake kaddamar da sabon samfurin solar mai suna FusionSolar a karshen makon jiya, daraktan kamfanin na Huawei a Najeriya Mr. Ni Zhilin ya ce, sabon makamashin samar da wuta ta amfani da hasken rana shi ne ya fi dacewa a Najeriya kasancewar yanzu duniya ta sauya zuwa amfani da wannan hanya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Mr. Ni Zhilin ya bayyana cewa, a yanzu haka kamar yadda bincike ya nuna Najeriya ita ce kasa mafi yawan amfani da injunan janareta wajen samar da wuta duk kuwa da tsadar man gas da man fetur da ake fuskanta, a don haka ya ce, ya zama wajibi ga ’yan Najeriya su rungumi tsarin amfani da wutar sola a matsayin mafita mai dorewa.

Da yake jawabi shugaban kungiyar masu masana’antu ta Najeriya reshen rukunin masana’antu na Bompai da kuma Jigawa Alhaji Mohammad Bello Umar cewa ya yi, karancin wutar lantarki ya kasance babban kalubalen da yake ciwa masana’antu tuwo a kwarya a Najeriya.

“Kowa a duniya ya san Huawei, ya san yadda kasar China ta yi suna wajen technology da kayan solar, muna murna da zuwan kamfanin nan, kuma mu kungiyar masu masana’antu kullum burin mu shi ne mu hada kai da kamfanin da ba zai kawo jabun kaya ba, kamfani kwararre, kamfani wanda aka sani a duniya kuma kamfanin Huawei Alhamdulillah kowa ya san shi, kowa aka ce fasaha ta solar da batira kowa ya san kamfanin Huawei saboda haka muna murna sosai da zuwansu jihar Kano.”

Ya zuwa yanzu dai kamar yadda manajan lura da sha’anin ayyuka na kamfanin a Najeriya Mr Jeremiah Ejiroghene ya bayyana, kamfanin na Huawei ya hada gidaje sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai da hasken wuta a sassa daban daban na duniya. (Garba Abdullahi Bagwai)