logo

HAUSA

Shirye-shiryen gasar U17 ta UFOA yankin B: ’Yan wasa Mena ’yan kasa da shekaru 17 sun shirya domin wakiltar Nijar

2024-05-13 09:56:45 CMG Hausa

’Yan wasan Mena na ’yan kasa da shekaru 17, za su halarci daga ranar 15 zuwa 28 ga watan Mayun shekarar 2024 gasar U17 ta UFOA yankin B, a birnin Accra na kasar Ghana. Cikin tsarin shirye-shiryen wannan gasa, matasa ’yan wasa talatin aka tattara a cibiyar bada horo ta kungiyar kwallon kafa ta kasa FENIFOOT da ke birnin Yamai.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Tun yau da ’yan makwanni suke samun horo da kulawa bisa hange da bukatar kwararrun kungiyar FENIFOOT.

Hakika, wadannan matasa ’yan kasa da shekara 17 sun fara wasannin sada zumunta domin a tantance matsayin kwarewarsu da kuma sanin kalubalen da ke jiransu a nan gaba.

A yayin wannan gasa ta U17 da za ta gudana a kasar Ghana, ’yan wasan Mena za su kece reni tare da ’yan wasan Eperviers na kasar Togo, da ’yan wasan Golden Eagles na tarayyar Najeriya da kuma ’yan wasan Etalons na kasar Burkina Faso.

A cewar shugabannin kungiyar FENIFOOT, shirye-shiryen wannan gasa an fara su tun yau da ’yan watanni tare da kwanbalar zakulo gwanayen ’yan wasa, a yayin kwanbalar da ta hada dukkan kungiyoyin ’yan wasa na kasa baki daya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.