logo

HAUSA

Nijar ta tura matasa hudu domin halarta gasar farko ta kasa da kasa ta sada zumunta kan kwarewa a kasar Iran

2024-05-11 18:16:43 CMG Hausa

A ranar jiya Juma’a 10 ga watan Mayun shekarar 2024, kasar Nijar, ta gabatar da matasa hudu da za su halarci gasar karon farko ta kasa da kasa ta sada zumunta kan kwarewa, a karkashin jagorancin ministan sadarwa Sidi Mohamed Raliou a yayin wani bikin musamman da ya gudana a birnin Yamai tare da kasancewar baki da dama.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

A yayin wannan biki, minista Sidi Mohamed Raliou ya mika wa shugaban tawagar tutar kasar Nijar a hukumance, a gaban idon jakadan kasar Iran da ke Nijar, jakadan Nijar dake kasar Iran, darektocin ma’aikatun gwamnati, da kuma sauran baki.

A dunkule matasa ’yan Nijar su hudu ne ’yan takara da za su je su kare tutar Nijar a wannan gasar karon farko da jamhuriyyar kasar musulunci ta Iran ta shirya cikin bangarori hudu.

Matasan sun hada da Oumboini Kondia Ounteni a bangaren fasahar web technologie, Souleymane Tidjiani Abdoul Hafiz a bangaren fasahar graphic design, Saidou Babaro Abdoul Kader a bangaren bunkasa mahajoji na salula da Abasse Hassane Raynatou a bangaren fasahar network system.

Ministan sadarwa Sidi Mohamed Raliou dake wakiltar faraminista Ali Mahamane Lamine Zeine da farko ya jinjina da bada kwarin gwiwa ga wadannan ’yan takara kafin ya yi kiransu ga yin aiki tukuru domin wakiltar Nijar yadda ya kamata.

“Faraminista ya dora mini nauyin wakiltarsa a nan domin isar muku da goyon bayansa gare ku hudun da za ku halatar wannan gasa a matsayinku na ’yan takarar Nijar. Mun yarda da ku, kuma an zabe ku daga cikin kwararrun matasa masu basira da hazaka, ke nan ku kasance masu kishin kasa, domin wakiltar kasarku, dukkan ’yan Nijar baki daya suna tare da ku kuma suna goyon bayanku”, in ji minista Sidi Mohamed Raliou.

A nasa bangare, darektan ma’aikatar tsaron internet, shugaban tawagar, Ali Soumana Abdourahamane, ya bayyana cewa tsarin tantance wadannan ’yan takara domin su wakilci Nijar ya bi sharudan kasa da na gogayyar kasa da kasa, kisa kwarewarsu ne aka zabe su.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.