logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya bayar da umarnin ci gaba da tsara aikin hanyar da ta tashi daga Badagry zuwa Jihar Sokoto

2024-04-30 09:24:27 CMG Hausa

Ministan ayyukan a tarayyar Najeriya Injiniya David Umahi ya ce, shugaban kasa Tinubu ya amince da a cigaba da tsara aikin babbar hanyar da ta tashi daga Badagry a jihar Legos dake kudancin kasar zuwa jihar Sokoto a arewaci, a wani mataki na fadada harkokin tattalin arzikin kasar.

Ministan ya tabbatar da hakan ne a ranar Lahadi 28 ga wata lokacin da ya kai ziyarar duba aikin hanyar Legos zuwa Calaba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Ita dai wannan hanya mai nisan kilomita dubu 1, an fara yinta ne tun a shekara ta 1978, amma aka dakatar da ci gaba da ita a 1979, kuma tana cikin tsarin taswirar ci gaban kasa a wancan lokaci.

Kamar yadda aka tsara dai, hanyar za ta ratsa wasu yankunan jihohi 12 ne wadanda suka hada da Lagos, da Ogun, da Oyo, da Abeukuta, da Kwara, da Niger, da Kebbi, ta kuma kare a Sokoto.

Ha’ila yau hanyar za kuma ta bi ta wasu kasashe makwafta kamar Benin, da Togo da kuma Jamhuriyar Nijar.

“Mun fara tsara yadda aikin zai kasance, kuma da zarar majalissar zartarwa ta kasa ta amince, za mu fara aikin daga yankin Sokoto.”

Ministan ayyukan ya ce, gwamnatin tarayya ta himmatu sosai wajen gina hanyoyin mota da suka ratsa yankunan da suke kusa da gabar teku a shiyyar kudu maso yamma, da kudu maso kudanci da arewa maso yamma da kuma shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya.(Garba Abdullahi Bagwai)