Shugaban tarayyar Najeriya ya kawo shawarar kai daukin gaggawa ga yankunan dake yankin Sahel domin ceto tattalin arzikin su
2024-04-29 14:23:21 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya ya bukaci manyan kasashen duniya masu karfin arziki da a ko yaushe su rinka la’akari da raunin kasashen Afrika musamman wadanda ke yankin Sahel wajen kai daukin rayuwa da na tattalin arziki.
Ya bukaci hakan ne jiya Lahadi a jawabinsa yayin babban taron duniya kan tattalin arziki da yake gudana a birnin Riyad na kasar Saudiya, ya ce hakika tattalin arzikin kasashen Afrika na fuskantar barazana sosai, kama daga na rikice- rikice da kuma na karuwar yawan jama’a.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce duk da dai akwai kasashe da dama da suke yin namijin kokari wajen daidaita tsarin tattalin arzikinsu ta hanyar samun shawarwarin kwararru na kasa da kasa, amma dai akwai bukatar sake samun kulawa ta musamman daga kasashe masu karfin arziki na duniya.
Ya ce a baya Najeriya ta shiga cikin jerin irin wadannan kasashe, amma sakamakon bullo da wasu dabarun farfado da tattalin arziki da gwamnatinsa ke kan yi a yanzu haka, al’amuran sun fara daidaituwa mutuka.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce kokarin maido da martabar Naira a kasuwannin duniya da fadada damammakin kafofin samun kudaden shiga tare da bullo da hanyoyin dogaro da kai ga miliyoyin matasa kasar ta amfani da sabbin fasahohin zamani, ya taimakawa kasar sosai.
Shugaban wanda ya bayyana cire tallafin man fetur da ya yi a farkon gwamantinsa, da cewar babbar dabara ce da ta ceto kasar daga cin karo da kalubalen rashin kudade, ko da yake matakin kamar yadda ya fada ya taimaka wajen haifar da tsadar rayuwa ga ‘yan kasa amma dai abu ne mai wucewa, kuma za a ga alfanunsa ba da jimawa ba.
“Daga cikin alama ta jagoraci shi ne zartar da wani hukunci mai tsaurin gaske a lokacin da ya kamata a zartar, wanda kuma zai zamanto mafi dacewa ga kasarmu, mun san cewa jama’a da dama ne ke kokawa sakamakon ji a jikin su , amma fa gwamnati tana daukar irin wadannan matakai ne domin kare bukatun ‘yan kasa.”
Daga karshen shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya ta yi imanin cewa hadin gwiwar tattalin arziki da hada kai a tsakanin kasashe ya zama wajibi muddin ana bukatar samun kwanciyar hankali a duniya baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)