logo

HAUSA

AU ta bayyana matukar damuwa game da tabarbarewar tsaro a yammacin Sudan

2024-04-28 16:04:59 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana matukar damuwa, game da kara tabarbarewar yanayin jin kai da tsaro a birnin El Fasher na jihar arewacin Darfur a yammacin kasar Sudan.

Cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar a ranar Juma’a, mista Faki ya ce gungun mayaka na taruwa, ana kuma ganin tarin makamai a kusa da wannan birni na El Fasher, matakin da ke matukar barazana ga rayuka, da dukiyoyi, da harkokin rayuwar miliyoyin jama’a, kuma hakan na kara dagula hali mai wahala, na wanzar da zaman lafiya da ake ciki a yankin.

Jami’in ya kuma yi kira ga daukacin sassa masu ruwa da tsaki a Sudan, da su goyi bayan kokarin kwamitin manyan jami’an AU, dake nazari game da yanayin kasar ta Sudan, da kuma kokarin kiran taron share fagen tattaunawar siyasa tsakanin dukkanin sassan Sudan nan ba da jimawa ba.

A wani ci gaban kuma, a dai ranar Juma’ar, ofishin MDD mai lura da tsare tsaren ayyukan jin kai ko UNOCHA, ya bayyana damuwa game da shirye shiryen da mayaka ke yi na aukawa juna a yammacin Sudan, wanda hakan ke matukar tayar da hankali, tare da dakatar da tallafi ga dubban mutane mabukata, da haifar da mummunan yanayin rayuwa ga fararen hula.

Birnin El Fasher, fadar mulkin jihar arewacin Darfur a yammacin Sudan, na fama da yanayin zaman dar dar na yiwuwar dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnati na SAF da na dakarun musamman na RSF. (Saminu Alhassan)