logo

HAUSA

Bankin raya kasashen Afrika zai taimakawa Najeriya da dala miliyan 134 domin habaka noman masara da shinkafa

2024-04-28 09:36:37 CMG Hausa

Bankin raya kasashen Afrika ya tabbatar da cewa, zai taimakawa Najeriya da tsabar kudi har dala miliyan 134 domin noman shinkafa da masara da waken suya da kuma rogo.

Shugaban bankin Mr Akinwumi Adesina ne ya tabbatar da hakan a karshen makon jiya lokacin da ya kai ziyara cibiyar nazarin noma a wuraren da suke da kamfar ruwa dake  jami’ar Bayero a jihar Kano.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //////

Shugaban bankin raya kasashen na Afrika ya ce, a cikin wannan shekara ta 2024 bankin zai agazawa Najeriya ta samu girbe hecta dubu dari uku na masara da shinkafa, da kuma hecta dubu dari da hamsin na rogo, sai kuma hecta dubu 50 na waken suya.

Ya ce ko a cikin watan jiya na Maris bankin ya taimakawa Najeriya domin ta samu sukunin noma hecta dubu dari da goma sha takwas na sabon nau’in iri na alkama da yake da juriyar zafi da kuma hecta dubu dari da hamsin na masara.

“Bankin raya kasashe na Afrika ya taba taimakawa kasar Ethiopia da nau’in irin alkama dake jure zafi, inda a cikin shekaru uku kacal suka kasance masu wadatar alkama, lamarin da yanzu haka kasar ke cikin kasashen da suke fitar da alkama domin sayarwa a kasashen duniya.”

Ya yi fatan cewa Najeriya za ta ribaci wannan tallafi da bankin zai ba ta domin ita ma ta kasance cikin jerin kasashen da suka yi fice a fagen samar da abinci a cikin kasa da kuma kasashen waje.

Daga karshe Mr. Akinwumi Adesina ya yi alkawarin cewa, bankin zai samar da wasu kudaden ga cibiyar binciken harkokin noma dake jami’ar Bayero ta yadda za su rinka yin aikin hadin gwiwa tare wajen hasashen yanayi tare kuma da tattara bayanai da za su baiwa manoma damar kimtsawa sosai wajen tunkarar noma a kowanne irin yanayi. (Garba Abdullahi Bagwai)